Luke 10

Yesu Ya Aiki Sabaʼin da Biyu

1Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum sabaʼin da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga. 2Ya ce musu, “Girbi na da yawa, amma maʼaikata kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi Ubangijin girbi ya aikar da maʼaikata zuwa gonarsa. 3Ku tafi! Ina aikanku kamar tumaki cikin kyarketai. 4Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ma ku gai da kowa a kan hanya.

5“Saʼad da kuka shiga wani gida, ku fara da cewa, ‘Salama a gare ku mutanen gida.’ 6In akwai mutum mai salama a gidan, salamarku za ta kasance tare da shi, in kuwa babu, salamarku za ta koma muku. 7Ku zauna a wannan gidan, kuna ci kuna shan duk abin da suka ba ku, gama maʼaikaci ya cancanci albashinsa. Kada ku yi yawan sāke masauƙi, daga gida zuwa gida.

8“Saʼad da kuka shiga garin, kuma aka karɓe ku, ku ci ko mene ne da aka ajiye a gabanku. 9Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’ 10Amma saʼad da kuka shiga garin, kuma ba a karɓe ku ba, ku bi titi-titi ku ce, 11‘Ko ƙurar garinku da kuke manne a ƙafafunmu, mun karkaɗe muku. Duk da haka, ku tabbatar da wannan, “Mulkin Allah yana kusa.” ’ 12Ina dai faɗa muku, a ranan nan, za a fi jin tausayin Sodom fiye da wannan garin.

13“ ‘Kaitonki, Korasin! Kaitonki, Betsaida!’ Ai, da a ce a Taya da Sidon ne aka yi ayyukan banmamaki da aka yi a cikinku, da tuni sun tuba, suna zama cikin shashan makoki da toka. 14A ranar shariʼa, za a fi jin tausayin Taya da Sidon fiye da ku. 15Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani za ki sami ɗaukaka ne? Aʼa, za a hallaka ki.

16“Shi wanda ya saurare ku, ni yake saurara. Shi wanda ya ƙi ku, ni yake ƙi. Amma shi wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.”

17Mutum sabaʼin da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.”

18Sai ya amsa, ya ce, “Na ga Shaiɗan ya fāɗi daga sama kamar walƙiya. 19Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku. 20Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama.”

21A wannan lokaci, Yesu, cike da murna ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na yabe ka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima, da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. I, ya Uba, gama wannan shi ne nufinka mai kyau.

22“Ubana ya danƙa mini dukan kome. Ba wanda ya san Ɗan sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Ɗan, da kuma waɗanda Ɗan ya zaɓa ya bayyana musu shi.”

23Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a ɓoye, “Albarka ga idanun da suka ga abin da kuke gani.

24“Ina faɗa muku, annabawa da sarakuna da yawa sun so su ga abin nan da kuke gani, amma ba su gani ba. Sun so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”

Misali na Mutumin Samariya Nagari

25Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don ya gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?”

26Yesu ya amsa, ya ce, “Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?”

27Sai ya amsa, ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’, kuma ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ”

28Yesu ya ce, “Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu.”

29Amma domin ya kāre kansa, sai ya tambayi Yesu, ya ce, “Shin, wane ne maƙwabcina?”

30Yesu ya amsa, ya ce, “Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, ʼyan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa duka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa. 31Ya zamana wani firist ya bi kan wannan hanya. Da ya ga mutumin, sai ya bi gefe ya wuce abinsa. 32Haka ma wani daga kabilar Lawi, mai hidima cikin haikali, da ya zo wurin, ya gan shi, sai shi ma ya bi gefe ɗaya, ya wuce abinsa. 33Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa. 34Ya je wurinsa, ya ɗaɗɗaure masa raunukansa, saʼan nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa. 35Washegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin, ya ce, ‘Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.’

36“A ganinka, a cikin waɗannan mutane uku, wane ne maƙwabcin mutumin da ya fāɗi a hannun mafasa?” 37Masanin dokoki ya amsa, ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Yesu ya ce masa, “Je ka, ka yi haka nan.”

A Gidan Marta da Maryamu

38Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. 39Tana da ʼyarʼuwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa. 40Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ʼyarʼuwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!”

41Amma Ubangiji ya amsa, ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa. 42Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.”

Copyright information for HauSRK